Old school Swatch Watches
Click here to visit © IBN HUJJAH™ Wap enjoy visiting...
tallace tallace na musanman awannan shafi kashiga koina ba matsala
Click here to visit © OMAR FAROOQ™ Wap enjoy visiting...
click to S M SCoollogo com-6122402
Ameenujibga BlogHomeForum

Ameenu jibga wap
Follow @fabregasjibga Good
¤RAMADAN MUBARAK¤ASSALAM ALAIKUM¤ KUDINGA RUBUTA AMEENUJIBGAWAP.XTGEM.COM A FCBK¤TWITTER¤I.GRAM¤YAHOO¤XTGEM¤DOMIN KAUNA¤
2024-05-18
1

AN JINJINAWA SHEIKH BALA LAU

AN JINJINAWA SHEIKH BALA LAU
AN JINJINAWA SHUGABAN IZALA NA ƘASA BISA ƘOƘARINSA NA HAƊAKAN AHLUS SUNNAH NA DUNIYA DA SAMARMA KUNGIYAR HANYOYIN DOGARO DA KAI. Daga Abdullahi Salisu Faru An yabama Shugaban kungiyar nan ta wa’azin Musulunci watau Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Iƙamatis Sunnah Sheikh Abdullahi Bala Lau akan ƙoƙarinsa na haɗa kan musulmi Ahlus Sunnah da samar da cigaba mai ɗorewa ga kungiyar. Shugaban Izala na ƙaramar hukumar mulkin Maradun da ke jahar Zamfara kuma mataimakin shugaban kungiyar na jahar na ɗaya Alh. Abubakar Aliyu Ɗan Madamin Maradun yayi wannan yabo a wani rubutu da yayi a shafinsa na Facebook. Ɗan Madamin na Maradun ya ƙara da cewa “Tabbas ƙungiyar Izala (Jibwis) ta samu gagarumin cigaba sanadiyyar shugabanci mai inganci a lokacin Sheikh Bala Lau”, Ɗan Madami ya zayyano wasu ayyuka waɗanda yace kaɗan ne daga cigaban da shugaba Bala Lau ya kawo a lokacin jagorancinsa ciki har da haɗin kan musulmi Ahlus Sunnah na Africa da turai gaba ɗaya inda ake magana da murya ɗaya. Alh. Abubakar Aliyu Maradun Danmadami ya ƙara da cewa ” A lokacin shugabancin Bala Lau ne aka kashe kungiyanci a cikin Izala tare da buɗe ƙofofi ga duk Ahlus Sunnah ko ina yake, musamman ɗaliban da suka kammala karatu a jami’o’in musulunci da ke Madina, Masar, Malesiya, Sudan, Uganda da sauran ɗaliban ilimi daga sassa daban daban waɗanda suka kammala jami’o’in Musulunci”. Ɗan Madamin Maradun yace yanzu al’umma suna amfanuwa ga Da’awar Sunnah ta hanyar sauraren tashoshin da Izala ta buɗe wanda wannan cigaba ne mai ɗorewa tare da samarma ƙungiyar da kuɗaɗen shiga. Alh. Abubakar Aliyu ya godewa wasu daga cikin manyan malaman sunnah waɗanda suka bada gudunmawa sosai wajen samun nasara ga shugabancin Sheikh Bala Lau, ya ƙara da cewa, girman Sheikh Bala Lau da suka yi bai hana su cigaba da yi mashi biyayya ba. Yayi addu’ar neman gafara ga wasu malamai waɗanda suka rigamu gidan gaskiya irinsu Sheikh Rabi’u Daura, Dr Alhassan Sa’id Adam Jos, Sheikh Jafar Mahamoud Adam Kano, Sheikh Abubakar Mahamoud Gummi, Sheikh Bawa Main Shinkafa, Sheikh Sma’ila Idris Jos, Alh. Musa Mai Gandu da sauran malamai. Alh. Abubakar Aliyu Ɗan Madamin Maradun yayi addu’ar neman Allah ya ƙara ba Sheikh Bala Lau hangen nesa da tunanin cigaba da zaƙulo hanyoyin cigaban wannan kungiya ta mu mai albarka.
Thank's for reading my article AN JINJINAWA SHEIKH BALA LAU
Created at 2018-03-08 00:48:44
Tags: LABARAI

0 Rate upStar
Share: F T G
Back to posts
This post has no comments - be the first one! AN JINJINAWA SHEIKH BALA LAU
Hi dear if you like(love) this wapsite and you want yours to be create,design for little amount and earn money per month on your site today click HERE
Kujera33183980 1274480762685550 3635758363742044160 o
¤RAMADAN MUBARAK¤ KUDINGA RUBUTA ¤AMEENUJIBGAWAP.XTGEM.COM A FCBK¤TWITTER¤I.GRAM¤YAHOO¤XTGEM¤DOMIN KAUNA¤
FACEBOOK ARENA UPDATES domin samun tallafi bangaren facebook click HERE
2GO ARENA UPDATES,domin samun agaji akan 2goHERE
Online: 1 user
Today : 11 user
This Week : 229 user
This Month : 339 user
Total all : 21398 visitors
Forum
Blog About Us
Countat Us

ameenujibgawap.xtgem.com™
Site Owned By Ameenu fabregas Jibga
Design By IbnHujjah™
All Rights Reserved © 2018
Created By:AMEENU JIBGA WAP
Copyright © 2016 -
Click here to visit © AMEENU GLOBAL™ Wap enjoy visiting...